Hakkin mallakar hoto NASA Image caption Marigayi Rishi Kapoor

Kwana daya bayan mutuwar fitaccen jaruman fina-finan Bollywood Irrfan Khan, mun kuma samu rahoton mutuwar Rishi Kapoor bayan ya shafe shekara biyu yana jinyar cutar kansa.

Rishi Kapoor mai shekara 67 ya mutu ne a asibitin Sir HN Reliance Foundation da ke birnin Mumbai na kasar Indiya.

Matarsa ​​da Neetu Kapoor ce ke jinyarsa lokacin da rai ya yi halinsa, kuma dan'uwansa ​​Randhir Kapoor ne ya sanar da wannan rasuwa.

Shahararren tauraron, Amitabh Bachchan ya bayyana cewa ya kadu da wannan mutuwa a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tiwita:

"Rishi Kapoor .. ya tafi .. ya yi gaba .. Na banu!"

A shekarar 2018, Rishi Kapoor ya kamu da cutar kansa, wanda hakan ya sa ya tafi birnin New York kuma ya kwanta a asibiti tsawon fiye da shekara guda.

Amma ya koma Indiya cikin watan Satumba na 2019 bayan ya samu sauki.

Rishi Kapoor shi ne ɗan marigayi tauraron fim Raj Kapoor kuma yana da 'yan uwansa ​​Randhir, da Ritu Nanda da Rima Jain da kuma Rajeev Kapoor.

Ya yi fim dinsa na farko mai suna Bobby tare da Dimple Kapadia a 1973, an kuma gan shi a matsayin mai wasan kwaikwayon yara a fina-finai kamar Shree 420 da Mera Naam Joker.

Ya kasance cikin fina-finan masu farin jini da aka fitar kamar Amar Akbar Anthony, Laila Majnu, Rafoo Chakkar, Sargam, Karz, Bol Radha Bol da sauransu.

Ya kuma fito a wasu fina-finai Kapoor and Sons, D-Day, Mulk da 102 Not Out.